Tashar talabijin din Rusiya Al-yaum ta habarta cewa kungiyar ta'addancin nan ta IS ta bayyana kanta a kasar Dimokaradiyar Congo bayan wani harin ta'addanci da ta kai, sannan ta bayyana sunanta wulayar Afirka ta tsakiya dake a matsayin wani bangare na kungiyar ISIS.
Bayan kai mumunan hari da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar Congo takwas, kungiyar ta ISIS ta dauki alhakin kai harin.
Cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar IS din ta ce harin da aka kai kan iyakar jamhoriyar Dimokaradiyar Congo da kasar Uganda, aikin mayakan kungiyar ne.
Kafin wannan sanarwa dai, Shugaban jamhoriyar Dimokaradiyar Congon Felix Tshisekedi ya sanar da cewa bayan kashin da kungiyar ISIS ta sha a kasashen Iraki da Siriya, kungiyar na kokarin kafuwa a Nahiyar Afirka.
Da dama daga cikin shugabanin kasashen Afirka na ganin cewa goyon bayan da kungiyoyin ta'addanci musaman kungiyar IS ke samu daga kasar Amurka da wasu kasashen Yamma shi ne dalilin da ya sanya suka samu gindin zama a kasashen Afirka.